14 Oktoba 2020 - 08:02
Kata’ib Hizbullah Ta Sake Jaddada Aniyarta Na Fada Da Kasantuwar Sojojin Amurka A Iraki

Daya daga cikin dakarun sa kai na kasar Iraki da aka fi sani da Hashd al-Sha’abi sun ja kunnen Amurka da cewa a shirye suke su yi amfani da karfi wajen kawo karshen kasantuwar sojojin Amurkan a kasar Irakin matukar Amurkawan ba su fice cikin ruwan sanyi ba.

ABNA24 : Kungiyar ta Kata’ib Hizbullah ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da daya daga cikin kwamandojinta Abu Ali Al-Askari ya fitar a jiya Talata inda ya ce dakarun gwagwarmayar a shirye suke su ci gaba da gwagwarmayarsu ta amfani da makami wajen fada da kasantuwar Amurka a kasar.

Har ila yau sanarwar ta kirayi sauran dakaru da kungiyoyin gwagwarmayar da su ci gaba da zama cikin shirin ko ta kwana don fada da sojojin Amurkan kamar yadda kuma ta kiraye su da su shirya makamansu don kai hare-hare sansanoni da barikokin sojojin Amurka matukar bukatar hakan ta taso.

Wannan sanarwar dai tana zuwa ne a daidai lokacin da wasu rahotanni suke nuni da shirin da Amurkan take da shi na yakar kungiyoyin gwagwarmayar wadanda suke fada da kasantuwarta a Irakin a daidai lokacin da ake ci gaba da kiraye-kirayen wajibcin ficewar sojojin Amurkan daga Iraki,.

342/